Tsohuwar ministar Man Fetur Diezani Alison-Madueke, ta
bukaci Hukumar EFCC da Babban Lauyan Gwamnatin
Tarayya su biya ta diyyar Naira biliyan 100 saboda bata mata
suna.
A cikin karar da lauyan ta Mike Ozekhome ya shigar, Diezani ta bukaci kotun ta tilasta wa hukumar EFCC ta wallafa mata sakon ban-hakuri a cikin akalla manyan jaridu uku, kuma dole
jaridun su hada da Thisday da Punch da kuma The Sun, sannan a yi wallafar cikin kwanaki bakwai da yanke hukuncin kotu.
Ta ce wallafe-wallafen da EFCC ta yi a kan ta, ta yi su ne da nufin bata mata suna da tozarta ta da cin zarafin ta tare da maida ta abar dariya a idon duniya.
Diezani, ta ce ta shigar da karar ne a kan wasu sarkoki da kayan kwalliya da su ka kai na Dalar Amurka miliyan 40 da aka ce nata ne, saboda babu wata kwakkwarar hujja a kan haka har zuwa lokacin da kotu ta bada umarnin kwace su.
Ta ce a karshen wa’adin mulkin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ta kamu da cutar sankarar mama, inda aka garzaya da ita Ingila don ganin likita, kuma tun lokacin ta ke ci-gaba da samun kulawar likitoci a can.

