Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Diezani: EFCC Ta Kwace Zinaren Dala Miliyan 40

Diezani Alison Madueke , Tsohuwar Ministar Man Fetur

Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Legas, ta bada umarnin a kwace wasu tarin gwala-gwalai da wayar salula samfurin I-Phone mallakin tsohuwar ministar mai Diezani Allison Maduekwe tare da mika su ga gwamnatin tarayya.

Hukumar EFCC ta nemi kotun ta ba gwamnatin tarayya damar rike kayayyakin ne, sakamakon ta na zargin tsohuwar ministar ta saye su ne da kudaden sata.

Karanta Labaru Masu Kama: EFCC Ta Kwace Wasu Gidaje Mallakin Diezani Madueke

Lauyan hukumar EFCC Rotimi Oyedepo ya shaida wa kotun cewa, kayayyakin sun hada da wayar salula da gwala-gwalai da su ka hada da ‘yan kunne da sarkoki da agoguna da sauran su, inda ya ce darajar su gaba daya ta haura dala miliyan 40, kimanin naira biliyan 14 kenan.

Bayan sauraren bukatar lauyan EFCC, Alkalin kotun mai shari’a Nicholas Oweibo, ya yanke hukuncin mika wa gwamnatin tarayya kayayyakin a matakin wucin gadi, zuwa lokacin da tsohuwar ministan za ta amsa sammaci.

Karanta Labaru Masu Kama: An Daure Jami’in Hukumar Zabe Shekaru 6 A Gidan Yari

Har yanzu dai Diezani ta ki yarda ta dawo Nijeriya domin fuskantar kararrakin da hukumar EFCC ke yi mata, wadanda su ka danganci satar biliyoyin kudaden gwamnati a zamanin da ta rike da mukamin ministar man fetur.

Exit mobile version