Home Labaru DCP Abba Kyari Ya Cafke Wasu Manyan Masu Satar Mutane A Imo

DCP Abba Kyari Ya Cafke Wasu Manyan Masu Satar Mutane A Imo

1407
0

Wasu masu garkuwa da mutane su bakwai da aka kama kwanan nan, sun bayyana yadda su ka kashe wani Ba’Amurke a cikin jihar Imo a shekara ta 2017.

‘Yan ta’addan dai sun shiga hannun babban jami’in dan Sanda DCP Abba Kyari da ‘Yan Tawagar sa na musamman.

Wadanda aka kama kuwa sun hada wani Sunday Igwe, da Michael Ahmefula, da Oyebuchi Echefule, da Ndubusi Isaac, Victor Dagogo, da Chima Okoro da kuma John Edet.

‘Yan ta’addan dai sun tabbatar da cewa, su ne ke yin fashi da makami, kuma su kan tsare mutane a yankunan Imo da Abia da kuma Rivers.Jagoran ‘yan ta’addan Sunday Igwe, ya bayyana yadda su ka kashe wani sojan kasar Amurka da su ka taba kamawa, inda ya ce sun kashe Ba-Amurken ne bayan sun gano cewa ya na dauke da bindiga a jikin sa.

Leave a Reply