Home Labaru Dambarwar NBC: Za A Gurfanar Da Lai Muhamed A Gaban Kotu

Dambarwar NBC: Za A Gurfanar Da Lai Muhamed A Gaban Kotu

1265
0

Hukumar yaki da rashawa da nau’ukan zamba ICPC, ta ce za ta gurfanar da tsohon ministan yada larabai Lai Mohammed a gaban kotu, domin yin bayani a kan yadda Hukumar sadarwa ta kasa ta kashe naira biliyan 2 da rabi ta hanyar da bai kamata ba.

Ishaq Modibbo, Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Da Nau’ukan Zamba ICPC

Mai magana da yawun hukumar Rasheedat Okoduwa ta tabbatar da shirin gurfanar da tsohon ministan, a shari’ar da aka yi wa Shugaban hukumar sadarwa Ishaq Modibbo Kawu na kashe kudaden wajen bada kwangilar da ta saba wa ka’ida.

Tuni dai ICPC ta gurfanar da Kawu da wasu jami’an hukumar sadarwar a gaban kotu, inda ake tuhumar su da laifuffuka 12 ciki har da yaudarar ministan wajen amincewa da wani kamfani mai zaman kan sa domin yin kwangila.