Home Labaru Dambarwar Majalisa: Yadda PDP Ke Kokarin Hana Lawan Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Dambarwar Majalisa: Yadda PDP Ke Kokarin Hana Lawan Zama Shugaban Majalisar Dattawa

521
0
Sanata Ahmad Lawan
Sanata Ahmad Lawan

Jam’iyyar PDP na shirin zawarcin wasu ‘yan majalisun tarayya na jam’iyyar APC goma sha uku da nufin hana Sanata Ahmad Lawan zama shugaban majalisar dattawa.

Wata majiya ta ce biyu daga cikin sanatocin da PDP ta tuntuba ne su ka sanar da shugabannin jam’iyyar da tawagar yakin neman zaben Sanata Lawan kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Sanatoci biyu ne ake sa ran za su jagoranci takwarorin su na jam’iyyar PDP na jihohin Adamawa da Taraba da Ekiti da Bauchi da Gombe da Kano da Kebbi.

Rahotanni sun ambato wani jigo a majalisar dattawa ya na cewa, a halin yanzu Sanata Ahmed Lawan ne dan takarar da za a kawar ta hanyar amfani da tsare-tsare da dabarun da duniya ta amince da su.

Wani zababen sanata da ya yi ikirarin bai amsa gayyatar PDP ba, ya ce a dukkan majalisun tarayya na duniya, a kan yi amfani da kwarewa a aiki ne wajen zaben shugabanin majalisa. Don haka ya ce idan jam’iyya ta samu rinjaye a majalisa bayan zabe, jagoran sanatocin jam’iyyar ne ke zama shugaban majalisa.