Shugaban hukumar jin korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano Muhuyi Magaji Rimingado, ya ce babu wanda ya tunzura hukumar ta binciki yadda masarautar Kano ta sarrafa kudaden ta.
Rimingado, wanda ya zanta da manema labarai a ofishin sa, ya ce hukumar ba ta hada al’amurran ta da kowa wajen binciken da ta ke gudanarwa a kan masarautar bisa zargin kashe kudaden ba bisa ka’ida ba.
Ya ce hukumar ta na gudanar da aikin ta ne da kan ta bisa yadda sashe na 8 da 9 da 15 na dokar hukumar yaki da cin hanci da rashawa na shekara ta 2008 ta tanada.
A cewar sa, hukumar ta na aiki ne a kan rubutacciyar kara da korafe-korafen da ta samu daga al’umma bisa zargin kashe kudade ba ta hanyar da ta dace ba a masarautar.