Home Labaru Dambarwar Gidan Zoo: Ganduje Ya Bada Umurnin A Gudanar Da Bincike

Dambarwar Gidan Zoo: Ganduje Ya Bada Umurnin A Gudanar Da Bincike

301
0
Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Kwanaki kadan bayan bazuwar labarin hadiye naira miliyan 6 da dubu 700 da ake zargin wani goggon biri ya yi a gidan Zoo na Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada umurnin gudanar da bincike a kan lamarin.

Gwamnan, ya bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta yi bincike a kan lamurran da ya kai ga batan kudin.

Rahotanni sun ce, Ganduje ya umurci hukumar ta yi nazari sannan ta gano abinda ya haddasa wannan zargi, ta kuma tabbara da ta bankado duk abin da ke zagaye da al’amarin.

Wasu jami’an gidan Zoo na Kano sun bayyana cewa, su na zargin wani Gwaggon biri da sace miliyoyin kudaden, kuma har yanzu ba a san inda ya boye kudin ba, sai dai sun ce su na zargin da ya sace kudin hadiyewa ya yi.

Leave a Reply