Home Labaru Ilimi Dambarwa: Ba Za Mu Yarda A Sake Yi Wa Malaman Kaduna Jarabawa...

Dambarwa: Ba Za Mu Yarda A Sake Yi Wa Malaman Kaduna Jarabawa Ba NUT

109
0

Kungiyar Malaman Nijeriya NUT, reshen jihar Kaduna, ta ce
babu wani malamin Makarantar Firamare da zai sake zama
rubuta jarabawar cancanta da Gwamnatin Jihar ke kokarin
shiryawa.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban ta
Ibrahim Dalhatu da Mataimakin Babban Sakataren ta Adamu
Ango, kungiyar ta bada shawarar maimakon haka gwamnati ta
yi amfani da kudaden da ta ware domin tantance malaman wajen
horas da su.

Idan dai ba a manta ba, a watan Janairu na shekara 2018,
gwamnatin jihar Kaduna ta sallami malamai dubu 22, saboda
faduwa jarabawar cancanta da aka gudanar a shekara ta 2017.

A ranar 14 ga watan Yuli ne, gwamnati ta sanar da shirin sake
gudanar da jarabawar cancanta ga malaman firamare, domin
tabbatar da ingantaccen tsarin koyarwar da su ke yi a
makarantun jihar.

Kungiyar, ta ce rubuta jarrabawar cancantar ba shi ke nuna
kwarewar malami a bakin aikin sa ba.