Majalisar malamai ta jihar Kano, ta bukaci a rage yawan masallatai a fadin jihar saboda guje wa rarrabuwar kawuna da zukatan al’umma.
Majalisar, ta kuma yi Allah-Wadai da malaman da ke kaskantar da kawunansu ta hanyar bin son ran ‘yan siyasa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, bayan kammala wani taro da ta gudanar na kwanaki biyu a karshen makon da ya gabata.
Majalisar, ta kuma yi kira ga malamai da limamai su rika raya masallatai da karatuttuka da lakcoci baya ga tsaida sallah a cikinsu.
Taron, ya maida hankali ne a kan gudunmawar da malamai da limamai ke bayarwa wajen samar da tarbiya da inganta zaman lafiya, tare da dora al’amura bisa tushen shari’ar Musulunci.