Home Labaru Dalilina Na Juya Wa Buhari Baya – Buba Galadima

Dalilina Na Juya Wa Buhari Baya – Buba Galadima

386
0

Tsohon na hannun daman shugaban kasa injiniya Buba Galadima, ya zayyana dalilan sa na juya wa shugaba Buhari baya tare da goyon bayan Atiku Abubakar.

Buba Galadima ya zayyana dalilan ne, yayin da ya bayyana a gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa a matsayin shaida na farko da jam’yyar PDP ta gabatar.

Buba Galadima

Yayin da yak e bada shaida, Buba Galadima ya shaida wa kotun cewa, ya dawo daga rakiyar shugaba Muhammadu Buhari saboda rashin adalcin gwamnatin sa.

Duk da goyon bayan shugaba Buhari a manyan zabubbukan shekara ta 2003 da 2007 da 2011 da 2015, Buba Galadima ya ce a halin yanzu ya sauya sheka sakamakon gazawar tsohon aminin sa na cika alkawurran da ya daukar wa ‘yan Nijeriya yayin yakin neman zabe.

Sai dai Buba Galadima ya musanta zargin cewa, fushin rashin samun mukamin minista bayan samun nasara a zaben shekara ta 2015 ne ya juya wa aminin sa baya.

Leave a Reply