Home Ilimi Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron Ba – Kwankwaso

Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron Ba – Kwankwaso

79
0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce bai halarci taron Kungiyar Lauyoyin Nijeriya ba ne sakamakon wasu muhimman ayyuka da su ka sha gaban sa.

Wannan ya na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike wa kungiyar lauyoyin, wadda kakakin sa Abdulmumin Jibril Kofa ya wallafa a shafin sa na Facebook, inda Kwankwaso ya ba kungiyar hakuri bisa rashin samun damar halartar taron.

A cikin wasikar, Kwankwaso ya ce abokin takarar sa Bishop Isaac Idahosa ya fita kasar waje, shi ya sa bai tura domin ya wakilce shi a wajen taron ba.

Taron dai ya samu halartar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, da Peter Obi na jam’iyyar LP da kuma mataimakin dan takararar shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Kashim