Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dalilin Da Ya Sa Matawalle Ya Maida Sarkin Fulanin ‘Yandoto

Gwamnatin jihar Zamfara, ta sa hannun amincewa da janye dakatarwar da ta yi wa Sarkin ‘Yandoto Aliyu Marafa bayan ta dakatar da shi watanni 10 da su ka gabata.

Gwamnatin jihar Zamfara, ta sa hannun amincewa da janye dakatarwar da ta yi wa Sarkin ‘Yandoto Aliyu Marafa bayan ta dakatar da shi watanni 10 da su ka gabata.

An dai dakatar da Aliyu Marafa ne bayan jin labarin yadda ya naɗa jagoran ‘yan bindiga Ado Aliero sarautar Sarkin Fulanin ‘Yandoto.

Masarautar ‘Yandoto dai ta ce ta naɗa Aleru Sarkin Fulanin ne don a samu zaman lafiya, kasancewar haifaffen yankin ne ba baƙo ba.

Sakataren Gwamnatin jihar Zamfara Kabiru Balarabe, ya ce gwamanti ta maida Sarkin ‘Yandoto a kan mukamin sa bisa shawarar kwamitin bincike.

Ya ce kwamitin ya gamsu da cewa, Sarkin ya naɗa Aleru ne domin a samu hanyar da za a kawo ƙarshen ta’addancin da ake yi, amma babu wata manufa ko siyasa a cikin lamarin.

Exit mobile version