Home Labarai Daliban Kwalejin Ilimi Ta Shehu Shagari Sun Kashe Wata Daliba A Sokoto

Daliban Kwalejin Ilimi Ta Shehu Shagari Sun Kashe Wata Daliba A Sokoto

171
0

An kashe wata dalibar kwalejin ilmi ta Shehu Shagari da ke jihar Sokoto, bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Rahotanni sun ce, an kashe dalibar mai suna Deborah ne bayan an bukaci ta janye kalaman ta amma ta ki.

Wata majiya ta ce, Deborah ta furta kalaman batancin ne a dakin kwanan dalibai, sakamakon rashin jituwar da ya auku tsakanin ta da wasu dalibai.

daya daga cikin daliban da ta bukaci a sakaya sunan ta, ta ce an bukace Deborah ta janye kalaman ta amma ta ki, hakan ya fusata sauran dalibai Musulmai a kwalejin.

Majiyar ta ce, jami’an tsaron makarantar sun boye ta a ofishin su, amma fusatattun matasa su ka fi karfin su su ka kashe ta, sannan su ka kona gawar ta kurmus.

Tuni dai gwamnatin jihar Sokoto ta rufe makarantar kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Leave a Reply