Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dalibai Sun Bukaci Tinubu Da Gwamnoni Da Su Kula Da Sha’Anin Tsaro

Daliban Nijeriya sun bukaci zababben shugaban kasa Bola
Ahmed Tinubu ya tabbatar da ingantaccen tsaro tare da samar
da ingantaccen ilimi a gwamnatin sa.

Haka kuma, a cikin jerin bukatun da daliban su ka gabatar, akwai batun samar da tsayayyiyar wutar lantarki da dabarun yaki da yunwa da fatara da daukaka darajar Nijeriya ta hanyar amfani da kyawawan manufofi.

Galibin yaran Nijeriya dai su na gararanba a kan tituna, inda wasu ke fuskantar matsalolin damuwa da shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar mutane da fyade da tashin hankali da talauci da dai sauran su.

Daliban sun yi kira ga Bola Tinubu ya magance matsalar rashin tsaro, musamman a makarantu tare da samar da yanayin da daliban da su ka rasa matsugunan su za su koma makaranta.

Exit mobile version