Home Labaru Dakile Barazanar Tsaro: Gwamnan Jihar Katsina Ya Umarci Da A Rufe Wuraren...

Dakile Barazanar Tsaro: Gwamnan Jihar Katsina Ya Umarci Da A Rufe Wuraren Cajin Wayoyin Salula

105
0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya sanar da kakaba dokar rufe wuraren da ake cajin woyoyin hannu na kudi a kananan hukumomi 19 na jihar.

Gwamnan wanda ya sanar da wannan doka a lokacin kaddamar da kwamitin da zai tabbatar da an bi sabbin dokokin inganta tsaro sau da ƙafa da gwamnatin ta kafa a makon jiya, ya ce gwamnati ta yanke shawarar hakan ne domin kara datse da kafar ‘yan ta’adda ke amfani da ita wajen muzguna wa al’umma a jihar.

Leave a Reply