Rikici ya kaure tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Rivers, bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal ta kwace ikon karɓar harajin Jiki-Magayi na ‘VAT’ a Jihar Rivers daga hannun Hukumar Tara Haraji ta Kasa ta damƙa wa gwamnatin jihar.
Hakan ya sa nan da nan Gwamna Nysom Wike ya sanya hannu a kan dokar da Jihar za ta fara karɓar harajin VAT, kuma ta hana a riƙa ba Gwamnatin Tarayya haraji ta hannun hukumar tara haraji ta kasa.
Haka kuma, Kotun ta yanke hukuncin cewa, Gwamnatin Jihar Rivers ke da ikon karɓar duk wani haraji a fadin jihar ba Gwamnantin Tarayya ba.
Wanann hukunci kenan ya na nufin an hana Gwamnatin Tarayya karɓar kuɗaɗen haraji a jihohi.