Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Cututtukan Zuciya: An Gano Magani A Birtaniya

Doctor drawing ecg heartbeat chart with marker on whiteboard concept for healthcare and medicine

Wani binciken masana kiwon lafiya a birnin London na kasar Birtniya, ya gano wani sabon maganin hawan jinin da ke gaggawar saukar da jini baya ga magance matsalolin da suka shafi ciwon zuciya da akalla kashi 50 cikin dari.

Sabon maganin wanda aka sanyawa suna Polypill, jaridar lafiya ta Lancet ta bayyana cewa tsawon shekaru 20 kenan da samar da shi sannan aka fara gwajin sa a tsakankanin shekarun 2011 zuwa 2013 kafin fara amfani da shi a bana.

Cikin tarin mutane masu fama da matsalolin da ke da alaka da ciwon zuciya ko hawan jini da suka yi amfani da maganin kamar yadda aka umarce su, bayanai sun nuna cewa sun samu raguwar hawan jini da akalla kashi 70 yayinda masu fama da bugun zuciya ya ragu da kashi 57.

A cewar Farfesa Kausik Ray, na kwalejin Imperial da ke birnin London tsawon lokaci an dakatar da gwajin maganin kan mutane masu tarin yawa har zuwa lokacin da aka kammala gwaje-gwaje a bana.

Farfesa Kausik Ray,

Farfesa Ray, ya bayyana cewa sabon maganin na saukar da hawa jinin nan take fiye da aikin da tsaffin magungunan na hawan jini da ciwon zuciyake yi a kwanaki 90.

Wasu rahotanni sun nuna cewa farkon gwajin maganin na Polypill ya gudana ne kan wasu mutane dubu 7 masu shekaru tsakanin 50 zuwa 75 can a yankin Golestan na kasar Iran karkashin jagorancin Dr Reza Malekzadeh, na jami’ar kimiyya da ke birnin Tehran.

Exit mobile version