Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

CUTAR MASHAKO: MUTUM 216 SUN KAMU 40  SUN MUTU A NAJERIYA

Stethoscope on a printed sheet of paper

Cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya ta tabbatar da cewa mutum 216 ne cutar mashako (diphtheria) ta kama a jihohin Kano da Yobe da Lagos da kuma Osun.

Kamar yadda bayanan hukumar suka nuna  zuwa yanzun cutar ta kashe mutum 40 a jihohin Kano da Lagos.

Hukumar ta ce daga cikin mutanen da suka rasu Kano tana da 38 yayin da Lagos take da biyu, haka kuma hukumar ta ce mutanen da suka kamu da rashin lafiya wadanda ake ganin ko cutar ce ta kama su yanzu sun kai 523 a jihohi biyar da suka kunshi Kano da Yobe da Katsina da Lagos da kuma Osun.

Shugaban kwamitin kwararru da ke yaki da cutar ta mashako a hukumar ta NCDC, Dr Bola Lawal, shi ne ya gabatar da wadannan bayanai a wani taro ta intanet a jiya Litinin.

Dr Lawal ya ce hukumar ta tashi tsaye wajen taimaka wa kwararrun da ke aikin yaki da cutar a jihohin da ta bayyana na Kano da Katsina da Yobe da Lagos da kuma Osun.

Exit mobile version