Home Home Cutar Mashaƙo Ta Kashe Ƙananan Yara Uku A Kaduna

Cutar Mashaƙo Ta Kashe Ƙananan Yara Uku A Kaduna

149
0

Cutar Mashaƙo ta hallaka ƙananan yara uku, tare da kwantar da wasu bakwai a asibiti, bayan ɓarkewar ta a ƙaramar hukumar Maƙarfi ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun ambato sakataren lafiya na ƙaramar hukumar Makarfi Malam Aliyu Alassan ya na tabbatar da hakan yayin zanatawa da manema labarai, inda ya ce an samu ɓuallar cutar a garin Tashar Na-Kawu da ke mazaɓar Gubuchi a ƙaramar hukumar.

Aliyu Alassan, ya ce mafi yawan waɗanda cutar ta kama ƙananan yara ne, amma tuni an ɗauki samfurin jinin su tare da aika shi Abuja domin yin gwaji saboda a tantance cutar.

Ya ce tuni an kai waɗanda ake zargin sun kamu da cutar zuwa asibiti, tare da killace su domin a ba su kulawar da ta dace.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna dai ta tabbatar da ɓullar cutar a wasu garuruwan Kafancan da ke yankin ƙaramar hukumar Jema’a, bayan bayyanar alamomin cutar a wasu unguwanni na garin kafancan.

Leave a Reply