Home Labaru Kiwon Lafiya Cutar Kwalara Ta Kashe Tubabbun ‘Yan Boko Haram 25

Cutar Kwalara Ta Kashe Tubabbun ‘Yan Boko Haram 25

55
0

Rahotanni daga yankin arewa maso Gabashin Nijeriya sun ce, akalla mutane 25, ciki har da mayakan Boko Haram 20 ne su ka mutu, sakamakon barkewar cutar kwalara a sansanin mahajjata da ke Maiduguri, inda yanzu haka kimanin mayakan Boko Haram dubu 12 da su ka mika wuya ke zama.

Wasu majiyoyi sun ce, akalla mutane dubu 1 suka kamu da cutar ya zuwa yanzu, wadanda kuma su ke karbar magani.

Sai dai wani jami’in ma’aikatar lafiya ta jihar Borno, ya ce tubabbun mayakan Boko Haram 11 ne kawai da wasu mutane uku a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Garage su ka mutu sakamakon cutar ba mutane 20 ba.

Wata majiya ta ce, ma’aikatan lafiya su na kokari tare da taimakon kungiyoyi masu zaman kan su da hukumar lafiya ta duniya, domin shawo kan lamarin ta fuskar rage yawan mace-mace.