Home Labaru Kiwon Lafiya Cuta: Kwalara Da Sankarau Na Kashe ‘Yan Nijeriya

Cuta: Kwalara Da Sankarau Na Kashe ‘Yan Nijeriya

208
0

Hukumar hana yaduwar cututtuka tare da samar da rigakafi ta Najeriya ta ce ‘yan Nijeriya 156 suka mutu a sanadiyar cututtukan Lassa, sankarau, da kuma kwalara tun daga farkon wannan shekarar ta 2019.

Hukumar ta ce tun farkon wannan shekarar annobar zazzabin cutar Lassa, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 110, wadanda aka tabbatar daga jihohi 21 suke tun daga 10 ga watan da muke ciki.

Hukumar ta ce jihohin da abin ya shafa sun hada da Edo, Ondo, Imo, Delta, Oyo, Bauchi, Nasarawa, Ebonyi, Plateau, Taraba, Kaduna, da Babban birnin tarayya Abuja.

Sauran sun hada da Adamawa, Gombe, Kwara, Benue, Ribers (Fatakwal), Kogi, Enugu, Kebbi da kuma Cross Riber.

Ta ce daga cikin mutanen da suka mutu akwai ma’aikatan lafiya 15, a jihohi 7, ya yin da daya daga cikin su ya mutu.

Dangane da cutar sankarau Hukumar ta ce gwaje-gwajen baya-bayan nan ya tabbatar da kamuwar mutane 17, sai kuma wasu mutane 27 da suka mutu daga jihohi 14, tun daga 3 ga watan Maris ne.

Wani babban jami’ai na bangaren daya shafi bincike na dakin gwaji, akan cuttuttukan da ke yaduwa, ya ce an samu karuwar barkewar annobar wannan shekara, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata 2018.