Home Home Cushen Kasafi: An Kara Naira Biliyan 206 a Kasafin Ma’aikatar Jinkai –...

Cushen Kasafi: An Kara Naira Biliyan 206 a Kasafin Ma’aikatar Jinkai – Sadiya Farouq

122
0

Ministar ma’aikatar jin-ƙai a Najeriya ta yi zargin cewa an yi mata cushen naira biliyan 206 a kasafin kuɗin ma’aikatarta.

A lokacin wani zaman kwamitin kula da ayyuka na musamman na majalisar dattawan ƙasar ranar Litinin, Sadiya Farouk ta nisanta kanta da zunzurutun kuɗin da ta ce an cusa a kasafin kuɗin ma’aikatar tata na 2023.

Sanata Elisha Abbo wanda mamba ne a kwamitin ya tambayi ministar game da kudin.

Kuma a martaninta ta ce ”Eh, mun ambato ayyukan da zamu yi da wannan kuɗi a kasafinmu na 2022 domin yin wasu ayyuka a ma’aikatar raya yankin Arewa maso Gabas. To amma ba a saki kuɗin ba, kuma sai gashi mun gan su yanzu an ninka yawansu sau 10.”

Ta ƙara da cewa ”za mu nemi bayani dalla-dalla daga ma’aikatar kuɗi kan yadda aka yi kuɗin ya ninka haka, duk da a baya ma ba a saki kuɗin domin yin ayyukan ba. Saboda haka za mu ji daga gare su sai mu dawo maku da bayani.”

A kan haka kwamitin ya ce zai gayyaci ministar kuɗi da kasafi, Zainab Ahmed domin ta bayar da bayani kan kuɗin naira biliyan 206 da Sadiya Farouq ta nisanta kanta da su.

Leave a Reply