Home Labaru Ilimi COVID-19: Nijeriya Za Ta Yi Amfani Da Sakamakon GCE Madadin WASSCE A...

COVID-19: Nijeriya Za Ta Yi Amfani Da Sakamakon GCE Madadin WASSCE A 2020 – Minista

422
0

Gwamnatin Tarayya, ta ce mai yiwuwa ta ce dalibai su rubuta jarabawar GCE a cikin watan Nuwamba, matukar aka kasa kammala shirye-shiryen rubuta jarabawar WASSCE, ta Afrika ta Yamma cikin lokacin da aka tsaida.

GCE dai jarabawa ce ta daban, wadda ake rubutawa a cikin watan Nuwamba, kuma a fito da sakamakon ta cikin watan Disamba.

Karamin Ministan Ilmi Emeka Nwajuiba ya bayyana haka, a wajen wani taron manema labarai da ya gudana a kan halin da ake ciki game da cutar Coronavirus a Nijeriya.

Minista ya ce canjin ya zama wajibi, ganin cewa babu wani dalilin da zai sa a kara wa’adin lokacin rubuta jarabawar WASSCE.