Cutar Coronavirus na kashe mutum 6 a duk sa’a 1 a kasar Iran a makon da muke ciki, a cewar alkaluman cutar COVID-19 da gwamanatin kasar ta fitar.
Faruwan hakan ya kai yawan wadanda cutar ta kashe zuwa mutum kusan 3,500 a Iran, wadda ke cikin jerin kasashen da annobar COVID-19 ta fi kamari.
Kawo yanzu mutum fiye da 50,000 ne suka kamu da cutar a Iran, duk da kokarin da gwamnatin kasar ke yi na dakile yaduwarta.
Cutar coronavirus ta yi ajalin manyan jami’an gwamantin Iran, ciki har da ministan lafiya da mataimakiyar shugaban kasar.
Yayin da cutar ke kara yaduwa a kasar, gwamnatin Iran na kara shan kakkausan suka kan matakanta na yakar cutar, musamman a birnin Qom, inda cutar ta fi kamari a kasar.
Sai dai wani mai sharhi kan siyasa kuma malami a Jami’ar Tehran, Mohammed Marandi, ya ce kasar ta kokarta wurin daukar mataki cikin gaggawa don shawo kan cutar tun sadda aka fara samun bullarta a kasar.
Marandi wanda ya ce shi ba mai goyon bayan gwamnati ba ne, ya ce takunkumin da Amurka ta kakaka ba wa Iran ya kawo wa kasar cikas wurin sayo kayan kula da lafiyar masu cutar daga kasashen ketare.
“Amurka ta yi amfani da bullar annobar a matsayin makami a kan mutanen Iran, ta hanyar haramta bangaren bankin Iran, da kuma sanya wa kamfanonin sarrafa magununa tsauraran sharuda ta yadda ba za su iya sayar wa Iran kayan asibiti ba.” Inji Marandi, a hirarsa da Aljazeera.
You must log in to post a comment.