Ya zuwa yanzu an samu karin mutum 2 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce Sabbin masu dauke da cutar sun shigo Najeriya ne daga; kasashen waje a kwana 7 da suka gabata.
Hakan ya sanya alkalumar masu cutar coronavirus karuwa zuwa 46 a Najeriya.

A sanarwar data fitar da safiyar Laraba, Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an samu karin masu cutar ne a jihohin Legas da Osun.
NCDC ta ce yaduwar cutar coronavirus da aka tabbatar a Najeriya ta takaita ne a jihohi kamar haka:
Legas- 30
Abuja- 8
Ogun- 3
Ekiti- 1
Oyo- 1
Edo- 1
Bauchi-1
Osun-1
Samun wanda ya harbu da cutar a jihar Bauchi shi ne karon farko da aka samu bullar COVID-19 a Arewacin Najeriya.
Duk da haka ba’a samu bullar cutar a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ba.
Kazalika babu labarin cutar a jihohin Kudu maso Kudu ba.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin WHO ta ce mutum fiye da 100,000 sun warke da cutar a fadin duniya, cikinsu har da mutum biyu a Najeriya.
You must log in to post a comment.