Home Labaru COVID-19: Zulum Ya Sa Dokar Hana Fita Na Kwana 14

COVID-19: Zulum Ya Sa Dokar Hana Fita Na Kwana 14

495
0
Covid-19: Gwamna Zulum Ya Kafa Dokar Hana Zirga-Zirga Na Tsawon Kwanaki 14
Covid-19: Gwamna Zulum Ya Kafa Dokar Hana Zirga-Zirga Na Tsawon Kwanaki 14

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ba da umurnin rufe jihar a wani mataki na hana yaduwar annobar coronavirus.

Zulum ya bayyana haka ne a cikin wani jawabi da ya gabatar, tare da cewa ya sa hannu a dokar ne sakamakon hadarin da  annobar ke da shi da lafiyar al’umma.

Dokar dai, ta haramta zirga-zirga a jihar na tsawon kwanaki 14, kuma ta fara ne daga karfe 10:30 na safiyar ranar Larabar da ta gabata.

Haka kuma, dokar ta ce daukacin al’umman jihar Borno su kasance a gidajen su, sannan za a rufe dukkanin ofishoshi da harkokin kasuwanci a fadin jihar.

Gwamnatin Zulum ta kara da cewa, za ta yi amfani da lokacin dokar wajen ganowa da killace mutanen da suka yi mu’amala da mutumin na farko da aka samu da cutar.

Sai dai, kwamitin jihar da ke yaki da yaduwar annobar COVID-19 ya gano mutane 97 da suka yi mu’amula da mai cutar wanda ya mutu. Shugaban kwamitin Umar Kadafur, kuma mataimakin gwamnan jihar ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya guda a Maiduguri

Leave a Reply