Home Labaru Covid-19: Ganduje Ya Maidawa Jigawa Yaran Da Ke Almajiranci A Jihar Kano

Covid-19: Ganduje Ya Maidawa Jigawa Yaran Da Ke Almajiranci A Jihar Kano

976
0
Covid-19: Ganduje Ta Maidawa Jigawa Yaran Da Ke Almajiranci A Jihar Kano
Covid-19: Ganduje Ta Maidawa Jigawa Yaran Da Ke Almajiranci A Jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta maida Almajirai 524 zuwa jihar jigawa a wani mataki na dakile yaduwar annobar covid-19.

Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ne ya karbi al’majiran da su ka kasance ‘yan asalin jihar sa a sansanin masu yi wa kasa hidima NYSC, inda za a duba lafiyar su kafin a mika su ga iyayen su.

Mai Magana da yawun gwamnan Auwal D Sankara ya bayyana haka a shafin san a yanar gizo, inda ya ce gwamntin jihar ta sha alwashin daukar dawainiyar al’majiran.

Kwamishinan ilmi na jihar Kano Sunusi Kiru, ya ce ba a amince Almajiran su shiga cikin gari ba har zuwa lokacin da aka tabbatar ba su dauke da wata cuta a jikin su.

Kawo yanzu dai an samu mutum guda da ya kamu da cutar COVID-19 a jihar Jigawa.