Home Coronavirus COVID-19: Gaduwar Farashin Danyen Mai Alheri Ne Ga Nijeriya – Atiku

COVID-19: Gaduwar Farashin Danyen Mai Alheri Ne Ga Nijeriya – Atiku

476
0
Faduwar Farashin Mai: Atiku Ya Bada Shawara
Faduwar Farashin Mai: Atiku Ya Bada Shawara

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce karyewar da farashin danyen mai a kasuwannin duniya alheri ne ga Nijeriya a fakaice.

Atiku ya ce, kamata ya yi Nijeriya ta kalli halin da kasuwar man fetur ta ke ciki a matsayin wata hanyar yayewa kan ta dogaro da man fetur.

Haka kuma, Atiku Abubakar ya ce, ya kamata faduwar farashin danyen mai a duniya ya kasance wani abun alfahari ga gwamnatin Nijeriya, kuma lokaci ya yi da ya kamata ta yi karatun ta natsu.

Farashin danyen man Nijeriya dai, bai yi faduwa irin ta sauran kasashe masu arzikin man fetur ba, amma har yanzu akwai rashin tabbas a kasuwar sa, musamman ganin yadda ake saida man na Nijeriya a kan dala 25 da digo 14 a kan kowacce ganga, sabanin yadda ake sayar da shi a bayan kafin bullar annobar Coronavirus a kan dala 45 zuwa dala 50 a duk ganga guda. Masana harkokin man fetur na ganin cewa, nau’in danyen man Nijeriya ya fi na sauran kasashe masu hako mai nagarta da inganci, saboda karancin sunadarin Sulfur da ya ke da shi.