Home Coronavirus COVID-19: El-Rufai Ya Kara Wa’adin Kwanaki 30 Na Zaman Gida

COVID-19: El-Rufai Ya Kara Wa’adin Kwanaki 30 Na Zaman Gida

470
0
COVID-19: El-Rufai Ya Kara Wa’adin Kwanaki 30 Na Zaman Gida
COVID-19: El-Rufai Ya Kara Wa’adin Kwanaki 30 Na Zaman Gida

Gwamnatin Kaduna ta kara wa’adin kwanaki 30 na zaman gida a wani makai na yaki da annobar Coronavirus a fadin jihar.

Gwamnan jihar Nasiru El-Rufa’i ya ce kara wa’adin na zuwa ne sakamakon shawarwari da kwamitin yaki da cutar ta bayar a karkashin mataimakiyar sa Dakta Hadiza Balarabe.

Yanzu dai gwamnatin jihar kaduna ta haramta fita a ranar Talata, maimakon a ranakun Talata da Laraba da aka saba fita domin sayan kayayyakin masarifi a baya.

Haka kuma, gwamntin kaduna ta wajabta amfani da ttakunkumin rufe fuska musammna ga wanda zai bar gida, sannan kuma dokar tazara za ta cigaba da aiki domin kawo karshen taruwar mutane a waje guda.

Gwamnatin kaduna ta ce babu maganar bude wararen ibada da gidajen biki da bude makarantu da kuma filayen wasanni da bude dakunan cin abinci, balantana gudanar da harkokin a tashoshin mota.

Haka kuma, babu maganar shigowa cikin jihar kaduna a wannan lokaci na yaki da annobar COVID-19, domin hukuma ba za ta lamucin hakan ba.

A karshe gwamnin ta ce za ta rage albashi masu ba gwamna shawara, sannan manyan jami’an gwamnati za su rika bada wani kaso daga albashin su domin a samu damar biyan kowane ma’aikacin jihar albashin sa.

Leave a Reply