Home Coronavirus Covid-19: An Soke Hawan Sallah A Masarautar Zazzau

Covid-19: An Soke Hawan Sallah A Masarautar Zazzau

689
0
Covid-19: An Soke Hawan Sallah A Masarautar Zazzau
Covid-19: An Soke Hawan Sallah A Masarautar Zazzau

Majalisar masarautar Zazzau sanar da cewa a bana ba za ta gudanar da bikin hawan Sallah  ba, kamar yadda aka saba yi a duk bayan kamalla azumin Ramadana.

Dan Isan Zazzau kuma mataimakin sakataren masarautar Alhaji Umaru Shehu Idris ya tabbatar da haka ga manema labarai, tare da yin kira ga al’ummar masarautar su kasance masu biyayya ga doka da oda.

Dan Isan Zazzau ya kara da cewa, kamar yadda gwamnatin tarayya da na jihohi suka soke duk wata hidima, ita ma masarautar zazzau ta dakatar da  hawan sallah domin hana taron mutane masu zuwa kallo daga wasu jihohin da ma kasashen ketare.

Alhaji Umar Idris ya bukaci alumma su yi hakuri da wannan matakin da masarautar ta dauka, saboda an yi haka ne domin kare lafiyar su.

Masarautar ta kuma shawarci mutane su cigaba da kiyayye kan su daga kamuwa da annaobar COVID-19, ta hanyar bin shawarwarin hukumomin lafiya.