Jami’an tsaro sun kama wasu motocin dakon kaya da aka boye mutane da ake kokarin fasakwabrinsu zuwa jihar Kaduna.
An boye mutanen ne a cikin dabbobin da motocin suka dauko domin yin basaja wajen shigo da su Kaduna.
A baya an yi ta samun zargin karya dokar rufe iyakokin jihar, wadda gwamnatin Nasir El-Rufai ta sanya domin dakile yaduwar annobar COVID-19.
Kazalika an samu rahoton yadda wasu mutane a jihohi ke karya dokar ta hana mutane taruwa da zumman takaita yaduwar cutar ta coronavirus.
Kwamishinan Harkokin Cikin Gida a jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya ce manyan motocin sun shigo Gwargwaji da ke Zaria a kokarinsu na shigowa Kaduna.
Samuel Aruwan ya kara da cewa, Gwamnatin jiahr karkashin Nasir El-raufai, ta yi nasarar gano mutanen tare da maida su inda suka fito, kamar yadda dokar jihar Kaduna ta tanada.
A cewarsa jami’an tsaro na aiki tukuru domin tabbatar da doka rufe iyakokin jihar kaduna, lamarin da yake ba su damar kama fasinjoji tare da tasa keyarsu zuwa inda suka fito.
Wannan dai, ba shine karo na farko da aka samu mutane a boye a cikin manyan motocin da ake kokarin shigo da su Kaduna daga jihar Kano ba.