Home Labaru Kiwon Lafiya Coronavirus: Majalisun Tarayyar Najeriya Sun Dage Zamansu

Coronavirus: Majalisun Tarayyar Najeriya Sun Dage Zamansu

532
0
Coronavirus: Majalisun Tarayyar Najeriya Sun Dage Zamansu
Coronavirus: Majalisun Tarayyar Najeriya Sun Dage Zamansu


Majalisun tarayya a Najeriya sun dage zamansu yayin da annobar coronavirus ke kara yaduwa a kasar.

A zamanta na ranar Talata ne Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila  ya sanar da dage zamanta sai abin da hali ya yi. 

Ita kuma Majalisar Dattawa, shugabanta Ahmad Lawan, ya ce sun dage zama zuwa ranar 7 ga watan Afrilu mai kamawa.

‘Yan majaliar sun kuma bukaci gwamantin tarayya ta dauki karin matakan kare yaduwar cutar coronavirus a kasar wadda hankula suka tashi a ciki game bullar cutar wadda zuwa yanzu ta yadu kasa fiye da 100.

A ranar Litinin wani sako da aka riya cewa ya fito daga ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, ya koka bisa yadda wasu ‘yan Majalisar Wakilai da ke dawowa daga kasashen ketare, suke kin yarda a yi musu gwajin cutar coronavirus a tashoshin jirage.

Hakan na zuwa ne yayin da Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ke cewa adadin masu dauke da cutar ya karu zuwa mutum 40.

Hukumomi a fadin kasar na kara daukar matakan kare yaduwar cutar, da suka hada da rufe makarantu da hana tarukan jama’a da umurtan kananan ma’aikata da su yi aiki daga gida, da dai sauransu.

Leave a Reply