Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya killace kansa saboda fargabar yiwuwar kamuwa da cutar COVID-19.
Hakan na zuwa ne a ranar da mutum na farko ya rasu a kasar sakamakon cutar da mutum 36 suka kamu da ita a kasar.
Gwaman da ‘yan tawagarsa sun killace kansu ne saboda hada jirgi da suka yi da dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda daga bisani aka gano ya kamu da cutar coronavirus
Da suke cikin jirgi, Bala Muhammad sun gaisa tare da shan hannu da dan gidan Atiku, wanda daga bisani Hukumar Hana Yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar ya kamu da cutar bayan dawowarsa daga kasar waje.
Sanarwar da ofishin gwamnan ya fitar, ta ce an dauki jinin gwamnan da ‘yan tawagar tasa domin gudanar gwaji, kuma gwamnan da ‘yan rakiyarsa za su kasance a killace zuwa lokacin da sakamakon gwajin zai fito.
Ofishin gwamnan ya fitar ya ce killace kai da gwamnan da ‘yan tawgarsa suka yi na daga matakan dakile yiwuwar yada kwayar cutar ga wasu mutane.