Hukumar kiwon Lafiya ta majalisar dikin duniya WHO ta shawarci mutane su rika amfani da naurorin zamani wajen bukatun kudaden su, domin mu’amala da kudi zai iya jawo yaduwar cutar corona.
Cutar Corona dai, za ta iya zama a kan kudi na tsawon kwanaki, matakin da ya sa dole a fadakar da mutane a kan wannan matsala domin kula da lafiyar su.
Mai Magana da yawun hukumar y ace, domin hana yaduwar cutar, wajibi ne mutane su rika amfani da naurorin zamani wajen gudanar da bukatun su na kudi, sannan su rika wanke hannayen su bayan sun taba kudi domin samun kariya daga kamuwa da cutar.
Wani
Bankin kasar Ingila ya gano cewa, takardun kudi na iya daukar kananan kwayoyin
cuta, wanda a watannin baya bankunan kasashe Koriya da China sun fara
tsaftacewa da killace kudaden da aka yi amfani da su domin takaita yaduwar
annobar cutar.