Home Labaru Kiwon Lafiya Cizon Sauro: Najeriya Na Kashe Sama Da Dala Biliyan 1 A Shekara

Cizon Sauro: Najeriya Na Kashe Sama Da Dala Biliyan 1 A Shekara

28
0
Screenshot 20240118 042634 Opera Mini
Screenshot 20240118 042634 Opera Mini

Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Pate, ya ce Najeriya na yin asarar sama da dala biliyan daya duk shekara sakamakon cutar zazzabin cizon sauro.

Muhammad Pate, ya bayyanna hakan ne, yayin kaddamar da taron bayar da shawarwari da tuntuba kan yaki da cutar ta zazzabin cizon sauro a Nijeria, wanda aka yi a nan Abuja.

A wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labaran ma’aikatar, Alaba Balogun, ya fitar, ya ce Pate, ya ce zazzabin cizon sauro ba matsala ce ta rashin lafiya ba kadai, ta zama matsala ga tattalin arziki.

Ya ce, cutar na ci gaba da yin gagarumar illa a kan Najeriya, inda ta ke da kashi 27 cikin dari na yawan mutanen da ke kamuwa da cutar a duniya.

Da kuma kashi 31 cikin dari na yawan mutanen da ke mutuwa a duniya a dalilin ta .

Ministan ya kara da cewa Najeriya ce ta fi fama da matsalar cutar, inda a 2022, sama da yara dubu 180, ‘yan kasa da shekara biyar suka mutu a sanadin cutar.

Ya koka da yadda cutar ke kassara kasa ta bangarorin lafiya da kuma tattalin arziki.

Leave a Reply