Home Home Cire Tallafin Man Fetur: Majalisar Tattalin Arziki Ta Najeriya Ta Gama Taro...

Cire Tallafin Man Fetur: Majalisar Tattalin Arziki Ta Najeriya Ta Gama Taro Ba Tare Da Cimma Matsaya Ba

118
0
Majalisar Tattalin Arzikin ta Najeriya ta kammala zamanta na farko a wannan shekarar ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ba tare da yanke shawara kan tallafin man fetur ba.

Majalisar Tattalin Arzikin ta Najeriya ta kammala zamanta na farko a wannan shekarar ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ba tare da yanke shawara kan tallafin man fetur ba.

Da manema labarai suka nemi jin abin da aka tattauna a taron sai ‘yan majalisar suka ɓuge da dogon bayanin suna cewa sun dade suna tattanauwa a kan batun, kuma sun samu bayanai masu yawa daga kwamitin da suka kafa, wanda Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufai ya jagoranta.

Wasu daga cikin bayanan sun nuna cewa farashin litar man fetur a dukkan kasashen da suka kewaye Najeriya ya ninka farashin da ake sayarwa a  najeriya  kuma a bara kadai Najeriya ta kashe fiye da naira tiriliyan biyu a kan tallafin mai.

Sun ƙara da cewa ba don tallafin mai ya lashe ba, da kudi ne da za a iya amfani da su wajen raya ilimi da samar da hanyoyin mota da asibitoci da sauran abubuwan more rayuwa.

Da yake Karin haske Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya faɗa wa manema labarai cewa bayan majalisar ta duba wadannan bayanan, sai ta fahimci cewa kasa da kashi daya bisa uku na jihohin Najeriya ne ke cin gajiyar kashi biyu bisa ukun tallafin man.

Leave a Reply