Home Home Cire Tallafin Mai: NLC Ta Sha Alwashin Yin Zanga-Zangar Adawa

Cire Tallafin Mai: NLC Ta Sha Alwashin Yin Zanga-Zangar Adawa

191
0
Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta ce za ta gudanar da zanga zanga a dukkan jihohin Najeriya domin adawa da shirin gwamnatin tarayyar na cire tallafin man fetur.

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta ce za ta gudanar da zanga zanga a dukkan jihohin Najeriya domin adawa da shirin gwamnatin tarayyar na cire tallafin man fetur.

Matakin kungiyar Kwadagon kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai dauke da sa hannun shugabanta Ayuba Wabba bayan taron majalisar zartaswar kolin da suka yi a Abuja a karshen mako.

A cikin watan Nuwamban da ya gabata, Ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed, ta bayyana shirin cire za’a cire tallafin man fetur, wanda ta ce za a maye gurbinsa da bayar da tallafin sufuri na naira dubu biyar ga masu karamin karfi akalla miliyan 40, domin rage musu radadin tasirin cire tallafin man.

Sai dai duk da haka kungiyar NLC ta sha alwashin  jagorantar zanga-zanga a dukkan jihohin Najeriya 36 a ranar 27 ga watan Janairun da ke tafe, yayin da kuma a birnin Abuja za ta yi gangamin a ranar 1 ga watan Fabarairu.

Batun cire tallafin mai a Najeriya ya sake tasowa a baya bayan nan ne, kasa da mako guda bayan da Hukumar ba da Lamuni ta Duniya IMF, ta baiwa gwamnatin Najeriya shawarar cire tallafin na man fetur domin karkata kudaden da take zubawa zuwa ayyukan raya kasa, inda shugaban kamfanin man NNPC Mele Kyari ya ce farashin man na iya kaiwa naira N320 zuwa N340 kowanne lita daga shekara mai zuwa.

Yayin da yake gabatar da jawabi a Abuja, Kyari yace tabbas babu abinda zai hana cire tallafin man a shekara mai zuwa, domin kuwa dokar da ake amfani da ita wajen biyan tallafin zata daina aiki daga karshen watan Fabarairu mai zuwa.

Leave a Reply