Shugabannin jam’iyyar APC, sun shaida wa shugaba Tinubu
cewa Nijeriya ta na farin ciki da shi bisa jajircewa da matakan
da ya ɗauka ya zuwa yanzu.
Da zuwan shugaban Tinubu a kan madafun iko dai ya dakatar da biyan kuɗin tallafin man fetur, sannan ya tsame hannun gwamnati daga harkokin musayar kuɗi da sauran matakai da dama da ya ɗauka.
‘Yan Nijeriya da dama sun koka da yadda ake fama da wahalhalu sakamakon tashin farashin man fetur, amma shugaba Tinubu ya tabbatar wa jama’a cewa wahalar ta wucin-gadi ce.
Da ya ke jawabi a wajen taron majalisar zartarwa ta kasa karo na 12 na jam’iyyar APC, muƙaddashin shugaban jam’iyyar na kasa Abubakar Kyari, ya yaba da matakan da shugaba Tinubu ya dauka.
Ya ce Nijeriya ta na cikin farin ciki da mulkin sa, bisa jajircewa wajen ɗaukar matakai masu tsauri.