Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Cire Tallafin Mai: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Amai Ta Lashe

Gwamnatin tarayya ta ce za ta ci gaba da bayar da tallafin man fetur a kasar nan , matakin da ke zuwa a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da fargaba kan yiwuwar kara farashin mai.

A ranar Litinin ne aka fitar da sanarwa da ke tabbatar da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta jingine shirin janye tallafin man fetur bayan wani taro da aka gudanar karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan.

Mahukunta a Najeriya dai sun yi bayani kan aniyarsu ta ci gaba da ba da tallafin man fetur a wannan shekara wanda tun a farkon wannan shekara ‘yan ƙasar nan suka shiga fargaba, sakamakon rashin sanya tallafin man fetur a kasafin kuɗin bana.

Mai taimakawa Sanatan kan hulda da jama`a, Bashir Hayatu Jantile, ya ce Sanata Ahmed Lawan, ya gayyaci masu ruwa da tsaki kan harkar man fetur inda ya nuna musu damuwarsa da sauran ‘yan majalisar da kuma shaida musu tattaunawar da ya yi da shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki.

A cewar Jantile, a wajen taron ne aka samu sabon bayani daga Ministar Kudin Najeriya a kan abinda gwamnatin tarayya ke yi game da batun tallafin man, wanda ake ta rade-radi game da janye shi.

Exit mobile version