Home Labaru Cire Tallafin Mai: Gwamnan Taraba Ya Rage Kuɗin Makaranta Da Kashi 50

Cire Tallafin Mai: Gwamnan Taraba Ya Rage Kuɗin Makaranta Da Kashi 50

105
0

Gwamnan Jihar Taraba Agbu Kefas, ya bada sanarwar rage
kuɗin makaranta na jami’ar jihar da kashi 50 cikin 100 domin
rage wa ‘yan asalin jihar raɗaɗin tallafin man fetur da aka
cire.

Mai magana da yawun Gwamnan Emmanuel Bello ya bayyana ma manema labarai haka a Jami’ar Jihar Taraba, inda ya ce batun ilimi ya na daga cikin muhimman fannonin da gwamnatin jihar za ta ba fifiko.

Ya ce tuni Gwamna Kefas ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimin jihar domin bunƙasa ilimi, kuma galibin ɗaliban jami’ar sun nuna jin daɗin su da wannan mataki da Gwamnan ya ɗauka, inda su ka ce hakan zai taimaka wa rayuwar su.

Emmanuel Bello ya kara da cewa, wasu iyayen yaran sun ce, mawuyacin halin da cire tallafin mai ya jefa su ya sa ba su iya biya wa yaran su kuɗin makaranta, amma yanzu rage kuɗin makarantar da Gwamnan ya yi zai ƙarfafa masu gwiwa.

Leave a Reply