Home Labaru Kasuwanci Cinikayya: Saudiyya Na Son Fara Shigo Da Nama Daga Najeriya

Cinikayya: Saudiyya Na Son Fara Shigo Da Nama Daga Najeriya

62
0
Abubakar kyari (1)
Abubakar kyari (1)

Gwamnatin Saudiyya ta bayyana buƙatar shigo da nama ton 200,000 da kuma ton miliyan ɗaya na waken soya daga Najeriya,

yayin da ƙasar ke son ƙarfafa cinikiyayya domin samun daloli, kamar yadda ministan noma na Najeriya ya bayyana.

Ministan noman ya ce Najeriya na son bunƙasa hulɗar cinikayya domin samun kuɗaɗen waje

musamman dala wanda zai taimaka wa ƙasar farfaɗo da darajar kudinta.

Najeriya ta daɗe tana neman rage dogaro da arzikin fetur zuwa wasu fannoni da za su taimaka wa tattalin arzikin ƙasar.

Ministan noman na Najeriya ya ce Saudiyya ta amince da buƙatar ne bayan ziyarar da ministanta na noma ya kawo a Najeriya,

kuma bayan tattaunawar, ƙasar ta aiko da buƙatarta.

Leave a Reply