Home Labaru Cin Zarafi: Sanata Abbo Ya Nemi Gafarar ‘Yan nigeria

Cin Zarafi: Sanata Abbo Ya Nemi Gafarar ‘Yan nigeria

333
0

Dan majalisar dattawa Sanata Elisha Abbo, ya nemi gafarar ‘yan Nijeriya game da cin zarafin da ya yi wa wata mata a wani shagon saida kayan batsa da ke Abuja.

Sanatan ya nemi gafarar ne yayin wani taron manema labarai da ya kira a helkwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja, inda ya ce ba halin sa ba ne tozarta mata, don haka ya yi nadama a kan abin da ya aikata.

Faifan bidiyon da ke dauke da yadda sanatan ya ci zarafin matar dai ya tada kura tare da janyo surutai a tsakanin masu fafutuka da dimbin ‘yan Nijeriya da fitattun ‘yan siyasa musamman a shafukan sada zumunta.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce ta fara gudanar da bincike a kan zargin cin zarafin matar da ake yi wa Sanatan.