Home Labaru Cin Zarafi: An Kama Wasu Katsinawa Uku Da Laifin Cin Mutuncin Buhari...

Cin Zarafi: An Kama Wasu Katsinawa Uku Da Laifin Cin Mutuncin Buhari A Yanar Gizo

1046
0
Kotu Ta Yi Wa Dattijon Da Ya zagi Buhari Da Masari Hukunci daurin watanni 18
Kotu Ta Yi Wa Dattijon Da Ya zagi Buhari Da Masari Hukunci daurin watanni 18

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane uku bisa zargin su da cin mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Aminu Bello Masari.

An dai kama mutanen ne bayan wani faifan bidiyo a shafukan sada zumuta na zamani ya nuna suna zagin shugabannin, wanda daga cikin su akwai wani dattijo dan shekaru 70 mai suna Lawal Abdullahi Izala, da Bahhajje Abu da kuma Hamza Abubakar, wanda dukkanin su mazauna unguwar Gafai ne da ke cikin garin Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah, ya ce an sanar da rundunar ‘yan sanda a kan faifan bidiyon da Lawal Abdullahi ya ke zagin Buhari da Masari, matakin da ya sa kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Sanusi Buba ya bada umarnin gudanar da bincike, tare da kama su.

SP Gambo Isa ya ce, mutanan uku sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa, lamarin da rundunar ‘yan sandan ta ce ba za ta lamunta ba.

A karshe rundunar ‘yan sandan ta ce, ba za ta nade hannu ta na kallon wasu tsirarun marasa tarbiyya su na sabawa dokokin kasa ba, tare da cewa duk wanda aka samu ya na amfani da dandalin sada zumun ta waje aibanta mutane zai yabawa aya zaki, kamar yadda aka tanada a karkashin dokokin hukunce-hukuncen manyan laifuka na yanar gizo.