Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta samu kaiwa wasan karshe na cin kofin Faransa wato French Cup bayan kwallon daya tilo da Kylian Mbappe ya zura a ragar Rennes daren jiya Laraba a wasan dab da na karshe da suka doka tsakanin su.
A minti na 40 gab da tafiya hutun rabin lokaci ne Mbappe ya zura kwallon bayan tun farko mai tsaron ragar Rennes Steve Mandanda ya buge fenaritin da tauraron na Faransa ya buga a minti na 33.
Mbappe wanda ke matsayin mafi zurawa PSG kwallo na taka leda ne a kakarshi ta karshe a kungiyar bayan amincewa da komawa Real Madrid ta Spain a kaka mai zuwa.
Kwallon ta Mbappe ta ba PSG damar kama hanyar yiwuwar lashe kofin na Faransa karo na 15, kuma karon farko bayan barar da damar su ta lashe kofin a 2021.
Haka zalika kungiyar ta PSG na kuma harin akalla kofuna 3 ne cikin wannan kaka da suka kunshi na Ligue 1 da zakarun Turai inda yanzu haka za ta hadu da Barcelona a wasan dab da na kusa da karshe.