Home Labaru Cin Amanar Ƙasa: An Kama Wasu Jami’An Tsaron Congo Da Laifi

Cin Amanar Ƙasa: An Kama Wasu Jami’An Tsaron Congo Da Laifi

114
0
20221003 232159
20221003 232159

Sojojin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sun kama wasu sojoji da jami’an ‘yan sanda da ake zargi da aikata laifin cin amanar kasa.

Babban hafsan tsaron ƙasar Janar Christian Tshiwewe Songesha ya fada ranar Litinin cewa an kama mutanen ne a Lubumbashi da Kinshasa amma bai yi ƙarin bayani ba.

Songesha ya sake nanata cewa sakamakon cin amanar kasa da doka ta tanada tare da bayyana irin azabar da sojoji ke fuskanta na rashin bayar da rahoton irin waɗannan ayyukan.

Ya ƙara da cewa shawarar da aka yanke na farfado da hukuncin kisa ga sojojin da ake zargi da cin amanar kasa ya kasance martani kai tsaye ga ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Gargadin na Janar Songesha ya biyo bayan rahotannin da ke cewa wasu ‘yan jam’iyyar tsohon shugaban ƙasar Joseph Kabila sun shiga sabuwar kawancen kungiyoyi masu dauke da makamai.

An kafa kungiyar Congo River Alliance, wadda ta haɗa da ƙungiyar ‘yan tawayen 23 a shekarar 2023 domin hamɓarar da gwamnatin shugaba Felix Tshisekedi ne.

Leave a Reply