Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara Ibrahim Dosara, ya ce hare-haren da sojoji ke kai wa ‘yan bindiga ya fara haifar da ɗa mai ido, sakamakon datse hanyoyin sadarwa a fadin jihar.
Dosara, ya bayyana haka ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Gusau, inda ya ce, a kokarin gwamnatin jihar na kawo ƙarshen ayyukan ‘yan bindiga, ta bukaci a katse dukkannin hanyoyin sadarwa na jihar, inda kuma ta samu haɗin kai nan take.
Ya ce, Jami’an tsaro sun samu sauki sosai wajen gudanar da ayyukansu na magance ‘yan ta’adda a maɓoyarsu da ke cikin daji.
Kwamishinan ya kara da cewa, sojojin sama sun yi ruwan bama-bamai a duk wasu sansanonin ‘yan bindigar da aka gano, inda daga bisani kuma na ƙasa suka shiga domin karasa waɗanda suka yi kokarin tserewa.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta ɗauki wasu matakan na daban, wanda ya yi daidai da irin bayanan sirrin da ta samu.