Home Labaru Cikar Obasanjo Shekaru 83: Atiku Ya Jinjinawa Tsohon Mai Gidan Sa

Cikar Obasanjo Shekaru 83: Atiku Ya Jinjinawa Tsohon Mai Gidan Sa

465
0
Cikar Obasanjo Shekaru 83: Atiku Ya Jinjinawa Tsohon Mai Gidan Sa
Cikar Obasanjo Shekaru 83: Atiku Ya Jinjinawa Tsohon Mai Gidan Sa

Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shekara ta 2019 Atiku Abubakar ya taya mai gidan sa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 83 a duniya.

Atiku Abubakar ya ce, idan aka bayyana Obasanjo a matsayin shakundum a siyasar Nijeriya ba a yi laifi ba, ko kuma wanda ya ke bin kasa bashi saboda na irin hidimar da ka yi mata.

Haka kuma, Atiku ya ce shi da iyalan sa suna taya Obasanjo murnar cika shekaru 83 a duniya, tare taya shi murna da Allah ya ba ka wannan dama.

Atiku Abubakar ya cigaba da cewa, babu wani dan Nijeriya da ke tafiya a ban kasa ko wanda ya rasu da ya kawo cigaba a siyasa kamar yadda Obasanjo ya kawo, tare da cewa dukkanin kasahen Afrika babu inda tambarin siyasar Obasanjo ba ta ratsa ba.

A karshe Atiku Abubakar ya ce, tsohon mai gidan sa Obasanjo shine mutum na farko da ya fara mika mulki a Nijeriya, sannan bayan shekaru 21 ya sake karbar mulki a farar hula, saboda haka jinjina a gare shi ta zama wajibi.