Home Labaru Ci-Gaban Kasa: Sarkin Musulmi Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Hada Kai Tare...

Ci-Gaban Kasa: Sarkin Musulmi Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Hada Kai Tare Da Fahimtar Juna

318
0
Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar
Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar

Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira dukkan shugabannin addini su kara kaimi wajen bunkasa rayuwar al’umma.

Sa’ad Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin nadin babban daraktan Hukumar Zakka na jihar Sakkwato Lawal Maidoki da aka nada a matsayin Sadaukin Sakkwato.

Mai alfarmar ya kara da cewa, Maidoki ya bada gagarumar gudummawa wajen kawo ci gaba a bangaren kungiyoyin addini da masu zaman kan su, tun lokacin da ya fara aikin gwamnatin har zuwa wannan lokaci. Saboda haka ya ke kira ga al’umma su tabbatar da cewa, sun fahimci junan su ta yadda za su amfani juna a kowa ne lokaci.