Home Labaru Ci-Gaba: Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Hukumar Raya Yakin Arewa Maso Gabas

Ci-Gaba: Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Hukumar Raya Yakin Arewa Maso Gabas

263
0
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce nan bada jimawa gwamnatin tarayya za ta kafa hukumar raya yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci jihar Borno domin kaddamar da wasu ayyuka a karkashin gwamnatin Kashim Shettima, wanda suka hada da makaratu da hanyoyin da wasu rukunan gidajen marayu.

Mataimakin shugaban kasa ya ce gwamnan jihar Borno Kashin Shettima ya cancanci yabo a kan irin ayyukan da gudanar, da kuma yadda ya jajirce wajen ganin an samu zaman lafiya a jihar.

A nashi bangaran Gwamna Kashim Shettima, ya ce mataimakin shugaban kasa na matukar kishin al’ummar jihar Borno, sakamakon yadda ya bigi kirji ya gina makarantar marayu a jihar.

Mai martaba shehun Borno Dakta Abubakar Garba Ibn Al-kanemi ya ce, akwai bukatar gwamnatin tarraya ta ba al’ummar jihar Borno dama wajen dibar su ayyuka da suka shafi jami’an tsaro duba da yadda irin wadannan ma’aikata suka rasa rayukan su a jihar sakamakon rikicin Boko Haram.

Leave a Reply