Home Labaru China: Zabtarewar Kasa Ta Janyo Mutuwa Mutane Da Dama

China: Zabtarewar Kasa Ta Janyo Mutuwa Mutane Da Dama

392
0

A kasar China akalla mutane 29 ne suka rasa rayukan su bayan wata zabtarewar kasa yayinda ake ci gaba da neman wasu 22 a wani kauye mai tsaunika dake da nisan kilometa dubu 2 da dari uku da babban birnin kasar.

Kasar China na daga cikin kasashe da lamarin zabtarewar kasa ke janyo mutuwar da dama daga cikin yan kasar.

A shekara ta 2017 kimanin mutane 141 suka bata sakamakon zabtarewar kasa da aka samu a kasar ta China da ya yi sanadiyar birne gidaje sama da 40 tare a wani gari dake lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar.

Al’amarin ya shafi yankin Sichaun, inda rahotanni suka ce zabtarewar ta janyo rusa gidaje da dama.

Gwamnatin kasar ta ware akala milyan 30 na kudin kasar a matsayin tallafi zuwa masu bincike ,kudin da za a yi amfani da su domin samarwa mutanen da suka rasa matsugunin wurin zama na gajeren lokaci.